Sojojin Najeriya sun kashe ‘yan bindiga shida a Kaduna

Spread the love

Dakarun runduna ta ɗaya ta sojin Najeriya sun kashe wasu ‘yan bindiga shida tare da kama wasu mutum uku a wani samame na musamman a ƙaramar hukumar Giwa da ke jihar Kaduna.

Cikin wata sanarwa da kwamishinan ma’aikatar tsaron cikin gida da harkokin cikin gida ta jihar Kaduna Samuel Aruwan, ya fitar ya ce sojojin sun samu nasarar kakkaɓe ‘yan bindigar bayan samun bayanan sirri kan ayyukan ta’addanci a yankin Galadimawa na karamar hukumar Giwa.

Sojojin sun kwato shanu tare da miƙa su ga mutanen yankin.

Daga nan ne sojojin suka hango maharan a dandalin kasuwar Galadimawa.

”Inda aka yi musayar wuta takanin ɓangarorin biyu, kafin daga bisani maharan su arce bayan kisan mutum shida daga cikinsu”, in ji sanarwar.

Bayan ƙaddamar da bincike a yankin ne kuma sojojin suka kama wasu mutum uku da ake zargi da hada baki tare da bai wa ‘yan bindigar bayai.

Sojojin sun kuma samu nasarar ƙwato babura biyu tare da wayoyin hannu huɗu a lokacin gumurzun.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *