Sojojin Najeriya sun kashe ƙarin fitaccen ɗanbindiga, Kachalla Makore

Spread the love

Gwamnatin jihar Zamfara ta tabbatar da cewar hukumomin tsaro a jihar sun hallaka ɗaya daga cikin riƙaƙƙun ƴan bindigar da ke addabar jihar mai suna Kachalla Makore tare da yaransa.

Gwamnatin ta ce an hallaka ɗanbindigar ne dai a lokacin da ya ke hanyarsa ta ɗauko gawar wani riƙaƙƙen dan bindiga da aka halaka a baya-bayan nan Kachal sani black a yankin Dan Sadau.

HHakan dai ya biyo bayan matakin da rundunar sojin Najeriya ta ɗauka na samar da wata rundunar Fansar Yamma, a tsakanin jihohin Sokoto, da Kebbi da Zamfara da Katsina don kakkaɓe ‘yanta’dda daga yankin.

Ko a kwanakin baya ma rundunar ta halaka gawurtacen ɗan bindigar nan da ya addabi jihohin Zamfara, Sokoto, Kastina da jihar Kaduna, Halilu Sububu, da karin wasu ’yan bindiga fiye da guda shida da suka addabi yankunan.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *