Sojojin Najeriya sun kashe ƴanbindiga sama da 1,000 a Agusta

Spread the love

Rundunar Tsaron Najeriya ta ce sojojinta sun kashe ƴan bindiga sama da 1,000 a cikin wannan watan a faɗin Najeriya.

Wannan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da Daraktan Rundunar Tsaron Najeriya, Manjo Janar Edward Buba, inda a ciki ya bayyana cewa aikace-aikacen sojin yana matuƙar daƙile ayyukan ƙungiyoyin ƴan bindigar.

“Muna sane cewa muna yaƙi ne da maƙiya marasa imani, wanda hakan ya sa dole mu ƙara ƙaimi wajen dakatar da su.”

Ya ce daga shirye-shiryen sojojin, akwai takura ƴan bindigar domin hana su sakat, “sannan sojojin suna bibiyar kwamandojin ƴan ta’addan da yaransu da ma masu taimaka musu.”

DANDALIN KANO FESTIVAL

Ya ƙara da cewa tuni sun ga bayan wasu manyan kwamandojin ƙungiyoyin a watan “A Arewa ta Gabas an kashe irin Munir Arika da Sani Dilla (Aka Dan Hausawan Jibilarram) da Ameer Modu da Dan Fulani da Fari Fari da Bakoura Araina Chikin da Dungusu da Abu Darda da Abu Rijab.”

Sanarwar ta kuma ƙara da cewa a yankin Arewa maso Yamma sojojin sun ga bayan manyan ƴan bindiga kamar su Kachalla Ɗan Ali Garin Fadama da Kachalla Ɗan Mani Na Inna da Kachalla Basiru Zakariyya da Sani Baka Tsine da Inusa Zangon Kuzi da Ibrahim da Tukur da Kamilu Buzaru da sauransu.

“Sojoji sun samu gagarumar nasara a kan ƴan bindigar, sannan kuma suna ci gaba da ƙara ƙaimi a aikace-aikacen da suke yi a yankunan Arewa maso Yamma da Arewa ta Tsakiya da Kudu maso Kudu da Kudu maso Gabas domin magance matsalar tsaron da ake fama da su.”

Ya ce jimilla a watan Agusta, sojoji sun kashe ƴan ta’adda 1166, an kama guda 1,096 sannan an tseratar da waɗanda aka kama guda 721.

Haka kuma a cewar sanarwar, ak ƙwato makamai 391, da alburusai 15,234, sannan sun daƙile satar mai da aka ƙiyasta ya kai na Naira biliyan 5.

“Aikace-aikacen sojojin sun sa ƴan bindigar sun ja baya sosai, wanda hakan ya sa suke ta miƙa wuya, musamman a Arewa maso Gabas,” in ji shi, sannan ya ƙara da cewa sojojin za su ƙara matsa lamba a sauran yankunan domin samun irin wannan nasarar.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *