Sojojin Najeriya sun kuɓutar da mutum huɗu da aka yi garkuwa da su a Kebbi

Spread the love

Rundunar sojin Najeriya ta ce ta kuɓutar da wasu mutum huɗu da aka yi garkuwa da su a jihar Kebbi da ke arewa maso yammacin Najeriya.

Wani samame da sojojin rundunar shiyya ta 8 suka kai sansanonin ƴan bindiga a ƙauyen Sabon Gari da ke karamar hukumar Shanga a yau Talata, tare da haɗin gwiwar jami’an tsaro na Cibil Defence da kuma ƴan sa-kai ne ya kai ga ceto mutanen.

Rundunar yan sandan Kano ta shirya tsaf don bayar da cikakken tsaro a ziyarar Uwar gidan shugaban kasa Oluremi Tinubu.

Yan Bindiga Na Shirye-Shiryen Kawo Min Hari — Dikko Radda

Wata sanarwa da mataimakin darektan yaɗa labaru na rundunar soji a Gusau, Kaftin Yahaya Ibrahim ya fitar, ya ce sun kuma samu nasarar kashe wani ɗan bindiga guda ɗaya.

Ya kuma ce sun yi nasarar ƙwato bindigogi da harsasai.

Sanarwar ta ce tuni mutanen da aka kuɓutar da suka kunshi maza huɗu, suka haɗu da iyalansu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *