Rundunar sojin Najeriya ta Hadarin Daji ta sake kuɓutar da mutum 52 da aka yi garkuwa da su a karamar hukumar Isa na jihar Sokoto.
Sanarwar da rundunar ta fitar, ta ce ta samu nasarar ceto mutanen ne a ranar Juma’a 22 ga watan Disamba, a ci gaba da samame da take yi a maɓoyar ƴan ta’addan.
Gwamnatin jihar Kaduna ta dauki nauyin nuna wasan Najeriya a wasu wurare
Gwamnatin jihar Oyo ta rufe coci saboda damun maƙwabta da hayaniya
Sojojin sun ce sun kuma samu nasarar kashewa tare da lalata wuraren da ƴan ta’ddan a kauyukan Saruwa, Kubuta, Gundumi da kuma dajin Bunwanga da ke jihar ta Sokoto.
Mutanen da aka kuɓutar ɗin sun haɗa da maza 14, mata 32 da kuma yara guda biyu.
Dakarun sun ce za a duba lafiyar mutanen kafin miƙa su ga hukumomi domin su sake haɗuwa da iyalansu.
Yansanda sun kama ƙasurgumin mai garkuwa da mutane a Abuja
Sojojin Najeriya sun sake gano wurin ƙera makamai a Plateau