Sojojin Najeriya sun lalata ‘masana’antar ƙera abin fashewa’ a tsaunukan Mandara

Spread the love

Rundunar sojin saman Najeriya ta ce ta lalata wani sansani da take zargin mayaƙan Boko Haram na ƙera abubuwan fashewa a tsaunukan Mandara da ke jihar Borno.

Cikin wata sanarwa da rundunar ta fitar ta ce, sakamakon yadda a baya-bayan nan mayaƙan Boko Haram ke amfani da abubuwan fashewa wajen kashe fararen hular da ba su ji ba su gani ba, musamman a jihar Borno, ya sa jami’anta suka tsananta bincike domin gano inda mayaƙan ƙungiyar ke ƙera abubuwan fashewar.

Sanarwar ta ce wasu bayanan sirri da sojojin suka samu sun bayyana mata cewa akwai wata masana’anta da ake ƙera abubuwan fashewar da kuma adana su a tsaunin Mandara.

Sojojin saman na Najeriya sun ce bayanan sun tabbatar mata cewa an sauya wa masana’antar matsuguni daga Gwoza zuwa Timbuktu a dajin Sambisa kafin dagabisani a mayar da shi yankin Grazah da ke tsaunin Mandara.

”Sakamakon tsananta hare-hare kan mayaƙan da sojoji ke yi a baya-bayan nan ya sa aka mayar da ɗauke masana’antar daga dajin Sambisa zuwa tsaunukan na Mandara”, in ji sanarwar sojojin.

Sojojin sun ce sun shafe tsawon makonni suna sanya ido kan wurin ƙera abubuwan fashewar da sauran ayyukan mayaƙan a yankin.

”A lokacin da muka ƙaddamar da harin, mun hangi wasu manyan motocin dakon makamai guda biyu a kusa da masana’antar, tsaye ƙarƙashin bishiya”, in ji sanarwar.

”Hakan ne ya sa ba mu yi wata-wata ba muka ƙaddamar da hare-hare a yankin, da nufin lalata masana’antar tare da kashe mayaƙan ƙungiyar”.

Sanarwar ta ci gaba da cewa sojojin sun samu nasarar lalata masana’antar.

Hotunan bayan harin sun nuna yadda wurin ya turnuƙe ta hayaƙi, bayan da masana’antar ta ƙone tare da motocin dakon makaman guda biyu.

SOJOJI , NIGERIA,

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *