Sojojin Najeriya sun sake gano wurin ƙera makamai a Plateau

Spread the love

Rundunar sojin Najeriya ta gano wata masana’antar ƙera makamai a jihar Filato.

Cikin wata sanarwa da rundunar ta fitar a shafinta na X, ta ce ta gano masana’antar ne a cikin tsaunukan ƙauyen Pakachi da ke yankin ƙaramar hukumar Mangu.

A lokacin samamen, sojojin sun ce sun samu makamai da wani kayayyakin ƙera makaman a masana’antar, tare da kama mutum guda da suke zargi da hannu a masana’antar.

Sanarwar ta ƙara da cewa rundunar sojin na farautar wanda ake zargi da mallakar masana’antar domin gurfanar da shi a gaban kotu.

Waɗansu ‘yan majalisa na son Najeriya ta koma tsarin firaminista

Rashin tsaro da yunwa mun san mafita aiwatar wa ce matsala :Sarkin Musulmi

Makaman da aka gano a masana’antar sun haɗar da:

  • Bindiga ƙirar AK 47 guda biyar.
  • Bindiga ƙirar gida 21
  • Ƙananan bindigogi 11 da harsasan su biyar.
  • Tukunyar sinadarin Carbide.
  • Saya guda uku.
  • Tarin nau’ikan harsasai daban-daban.
  • Guduma guda huɗu.
  • Mashina tono shida.
  • Injin janareto.
  • Da sauran abubuwa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *