Rundunar sojin Najeriya ta gano wata masana’antar ƙera makamai a jihar Filato.
Cikin wata sanarwa da rundunar ta fitar a shafinta na X, ta ce ta gano masana’antar ne a cikin tsaunukan ƙauyen Pakachi da ke yankin ƙaramar hukumar Mangu.
A lokacin samamen, sojojin sun ce sun samu makamai da wani kayayyakin ƙera makaman a masana’antar, tare da kama mutum guda da suke zargi da hannu a masana’antar.
Sanarwar ta ƙara da cewa rundunar sojin na farautar wanda ake zargi da mallakar masana’antar domin gurfanar da shi a gaban kotu.
Waɗansu ‘yan majalisa na son Najeriya ta koma tsarin firaminista
Rashin tsaro da yunwa mun san mafita aiwatar wa ce matsala :Sarkin Musulmi
Makaman da aka gano a masana’antar sun haɗar da:
- Bindiga ƙirar AK 47 guda biyar.
- Bindiga ƙirar gida 21
- Ƙananan bindigogi 11 da harsasan su biyar.
- Tukunyar sinadarin Carbide.
- Saya guda uku.
- Tarin nau’ikan harsasai daban-daban.
- Guduma guda huɗu.
- Mashina tono shida.
- Injin janareto.
- Da sauran abubuwa.