Sojojin Najeriya za su kama masu amfani da tufafin sojoji

Spread the love

Rundunar sojin ruwan Najeriya ta ce za ta fara kama mutanen da ke amfani da tufafin sojoji ba tare da izini ba.

Cikin wata sanarwa da kakain rundunar, Commodore A Adams Aliu ya fitar,ya ce tana gargaɗin mutane domin su fahimci abubuwan da doka ta tanada da kuma illar da ke tattare da amfani da tufafin sojoji ba tare da izini ba.

Matakin na zuwa ne bayan wasu rahotanni sun yi zargin cewa wasu mutane waɗanda ba sojoji ba sanya tufafin sojojin ba tare da izini ba.

“Ya zama dole mu tunatar da jama’a cewa yin amfani da tufafin sojoji ba tare da izini ba laifi ne, kamar yadda sashe na 12, ƙaramin kashi na 110 (1) da (2) na kundin aikata laifuka ya bayyana, laifi ne ga duk mutumin da ba ya aiki cikin rundunar sojin Najeriya, ya sanya tufafin sojoji ko wani abu da ke kama da tufafin,” in ji sanarwar.

Rundunar ta bayyana ƙarara cewa bin wannan umarnin na da matuƙar muhimmanci, kuma rashin bin umarnin na iya haifar da kamawa da kuma gurfanar da mutum a gaban kotu kamar yadda doka ta tanada.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *