Rundunar hadin gwiwa ta Operation UDO KA , ta samu nasarar dakile yunkurin yin garkuwa da wani mutum a yankin unguwar Umuaka da ke karamar hukumar Njaba ta jahar Imo.
Kakakin rundunar hadin gwiwa ta Operation UDO KA, Lt.-Col. Jonah Unuakhalu, ya bayyana hakan ne a wata sanarwa da ya fitar ranar Asabar a Enugu, inda ya ce dakarun da ke sintiri ne suka dakile yunkurin garkuwar a ranar 17 ga Mayu2024.
A cewar Unuakhalu, sojojin a lokacin da suke sintiri na yau da kullun a Umuaka, daura da hanyar Orlu zuwa Owerri, wadanda aka sanar da su, yunkurin garkuwa da mutane.
Ya ce: “Sojoji sun yi gaggawar bin sahun masu garkuwa da mutane tare da cin musu.
sojojin sun kashe daya daga cikin masu garkuwa da mutane tare da raunata wasu biyu .
“Sojojin sun kwato bindiga kirar AK 47 guda daya dauke da harsasai da kuuma babur.”
Kakakin ya ce haka ma, sojoji tare da jami’an rundunar sojin ruwa dake Oguta, sun kashe wani dan kungiyar ‘yan (IPOB) a kauyen Amagberedere da ke karamar hukumar Oguta ta jihar Imo.
- Sojoji Sun Yi Dirar Mikiya A Kasuwa Bayan Dukan Abokin Aikinsu.
- Kwamitin malaman addinin musulunci na Najeriya ya goyi bayan auren marayu a Neja