Jami’an tasro a Jamhuriyar Nijar sun yi nasarar cafke ƙasurgumin ɗanbindigar nan Ɓaleri, wanda ake nema ruwa a jallo a Najeriya.Dakarun runduna ta musamman da ake yi wa laƙabi da Farautar Bushiya (Faraoutar Bushiya), sun kama shi ne a garin Rigar Kowa Gwani, da ke yankin Gidan Rumji a jihar Maraɗi.
A sanarwar da hukumomin sojin Nijar suka bayar, sun ce an damƙe Ɓaleri ne da misalin ƙarfe 1 na yamma a lokacin ya yake wata ganawa da yaransa kan yadda za su kai hari Najeriya da Nijar.
Rahotanni sun ce Ɓaleri wanda ɗan asalin Shinkafi ne a jihar Zamfara, wanda ya tsere daga Najeriya , ya jima yana addabar jama’a a yankunan jihar ta Zamfara da kuma Maraɗi a Nijar.
Kuma makusanci ne ga ƙasurgumin ɗanbindigar nan da shi ma ya yi ƙaurin suna a arewacin Najeriya, Bello Turji.
Ɓaleri shi ne na 40 a jerin mutanen da hukumomin sojin Najeriya suka fi nema ruwa a jallo, inda aka sanya lada na musamman ga duk wanda ya kama shi ko ya bayar da labarin inda za a same shi.
- Rundunar Yan Sandan Kano Ta Ce Za Ta Tabbatar Da Umarnin Gwamnati Kan Hana Zanga-zanga
- Tinubu ya samu tarba da sabon taken Najeriya a majalisar dokokin ƙasar