Sojojin Sama Sun Kashe Yan Bindiga Sama Da 100 A Katsina

Spread the love

Hukumomi a jihar Katsina sun ce wani harin sojojin sama ya yi sanadin hallaka ƴan fashin daji sama da 100 da safiyar jiya Alhamis a ƙauyen Shawu na ƙaramar hukumar Faskari.

Bayanai sun ce lamarin ya faru ne bayan wani shiri da ƴanbindigar suka yi na kai wa jami’an tsaro hari a yankin.

Nasiru Ma’azu shi ne kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na jihar Katsina, ga kuma tabbatar da faruwar lamarin a zantawarsa da BBC.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *