Rundunar sojin saman Nijeriya ta bayyana cewa, harin da ta kai ta sama a karkashin rundunar ‘Operation Fansar Yamma’, a ranar Lahadi 10 ga watan Agusta, 2025, ta yi luguden wuta kan taron ‘yan bindiga 400 a lokacin da suke shirin kai hare-hare kan al’ummomi manoma a jihar Zamfara.
Kakakin sojojin, Air Cdre Ehimen Ejodame, a wata sanarwa da ya fitar, ya ce harin da aka kai ta sama da na kasa da aka kai dajin Makakkari, ya halaka ‘yan ta’adda da dama.
- An gurfanar da waɗanda ake zargi da harin cocin Owo bayan shekara uku
- Direba ɗaya ya tsira a hatsarin tankokin dakon iskar gas a Zariya
A cewar Ejodame, na’urar leken asiri ta tabbatar da zirga-zirgar ‘yan bindiga sama da 400 da ke shirin kai hare-hare kan al’ummomi manoma a lokacin da aka yi musu luguden wuta.
Kakakin NAF ya ce harin, an kai ne tare da hadin gwiwar runduna ta kasa, wanda ya yi sanadin mutuwar wasu fitattun ‘yan bindiga rundunarsu da dama.
Daraktan ya kuma jadadda cewa hadin kai tsakanin sassan sama da na kasa na Operation Fasan Yamma ya sa farmakin ya zama na musamman.