Waɗanda suka yi mining din Hamster Kombat sun koka matuka bisa yadda farashinsa ya fito babu daraja a ranar farko da ya fara shiga kasuwar cikifto.
Idan za a iya tunawa tun watanni 6 da suka gabata Matasa da dama a duniya suka fara harkar mining din Hamster Kombat da tunanin zai yi daraja a kasuwa.
A yau alhamis 26 ga watan Satumba da misalin karfe 1 na rana ne dai Hamster ya fashe wanda hakan yake nuna cewa ya shiga kasuwa domin yin hada-hadar shi a kasuwar Kirifto.
Hamster Kombat dai ya fito kowanne daya akan 0.01 wanda hakan ya fusata yan baiwa ma’ana waɗanda suka yi mining din Hamster Kombat.
- Ba Zan Lamunci Cin Hanci Da Rashawa Ba, Kudirat Kekereke-Ekun
- An Kai Tsohon Shugaban Sudan Omar al Bashir Asibiti