Spain ta hana tawagar Najeriya bizar zuwa wasanni – NFF

Spread the love

Ƙasar Spain ta hana ‘yan wasan tawagar Najeriya ta ‘yan ƙasa da shekara 15 bizar zuwa buga gasa ƙasar, kamar yadda hukumar kwallon ƙafa ta ƙasar NFF ta bayyana.

Hana bizar ya shafi ‘yan wasa da jami’an da ke cikin tawagar masu lura da su, kamar yadda NFF ta bayyana.

Don haka, “tawagar ba za ta je Spain ba domin buga gasar Uefa ta ‘yan ƙasa da shekara 16,” kamar yadda NFF ta wallafa a shafinta na X.

Spain dai ba ta bayyana dalilin hana bizar ba.

Sai dai hukumomin Spain sun ce dalilin da Hukumar NFF ta bayar na neman bizar bai yi “daidai ba”.

“Jami’inmu da ke Legas ya ce ya bi bayanan mutanen ya ga, wadanda suka nemi bizar a ranar 8 ga watan Afrilu sun janye buƙatarsu,” kamar yadda wani wakili ya shaida a ofishin jakadancin Spain a Najeriya.

“Babu wanda ya hana su biza”.

An tsara Future Eagles za ta bar Najeriya a ranar Talata domin gasar, kuma za ta fara wasanta na farko da Belgium ne a ranar JUma’a.

Kazalika za ta buga wasa da Ingila da Italiya a gasar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *