Sudan ta Kudu ta haramta giyar da ta hallaka dubban mutane

Spread the love

Hukumomi a jihar Equatoria ta Tsakiya da ke Sudan ta Kudu sun hana sayar da wata mashahuriyar giya bayan da mutane da dama suka mutu sakamakon shan giyar da suka yi a yankin.

Giyar wadda aka fi sani da “Makuei Gin” an ce galibi matasa ba sa iya jurewa sai sun sha.

An ba da rahoton cewa, yawan amfani da giyar ya karu a lokacin bukukuwan Kirsimeti da na sabuwar shekara, wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutane da ba a tantance adadinsu ba.

Kungiyar lauyoyi NBA ta kai karar Hannatu Musawa kan shedar bautar ƙasa NYSC

Babbar kotun Kaduna ta yanke wa mai garkuwa da mutane hukuncin shekaru 21 a gidan yari

“Na dakatar da amfani ko shan wannan jar giya mai suna ‘Makuei’. Na haramta sayar da ita ko shan ta domin tana kashe matasa da dama, “in ji gwamnan jihar Equatoria ta Tsakiya, Emmanuel Adil Anthony a ranar Lahadi.

Ya kara da cewa, “Matasa da yawa idan suka bugu, sai su rika dukan uwayensu da adduna.

Daliba Ta Kashe Kanta Saboda Lakcara Ya Daina Son ta.

Cocin Anglican da ke babban birnin ƙasar Juba, ta buƙaci gwamnan da ya tabbatar an aiwatar da dokar haramta giyar.

A shekarar da ta gabata ne ministan yaɗa labarai Michael Makuei ya yi kira da a haramta amfani da giyar sannan ya bukaci a rufe masana’antar da ke samar da ita.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *