Sudan ta nemi duka ‘yan ƙasar waje su fice daga birnin Khartoum cikin kwana 10, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Sudan (Suna) ya ruwaito a jiya Alhamis.
“Shugaban sashen ‘yan ƙasar waje da kuma shige da fice a Khartoum, Kanar Nizar Khalil, ya bai wa ‘yan ƙasar wajen umarnin fita daga Khartoum cikin kwana 10 domin kare tsira da rayukansu daga yaƙi,” a cewar rahoton na Suna.
Akasarin birnin na Khartoum – da ya haɗa da tsakiya da kuma biranen unguwannin Bahri da Omdurman – na ƙarƙashin ikon RSF, ƙungiyar da take ta yaƙi da dakarun gwamnatin ƙasar tun Afrilun 2023.
Gwamnatin ƙasar ta soja ta yi yaƙi da ‘yan ƙasar wajen da suka shiga ba bisa ƙa’ida ba, tana mai zargin su da taimaka wa ƙungiyar ta RSF.
A ranar 8 ga watan Yuli hukumomi sun tsare ‘yan ƙasar waje 154 da ake zargi sun shiga ta ɓarauniyar hanya. Sai dai RSF ta musanta zargin.