Sufeto Janar na ƴan sandan Najeriya Kayode Egbetokun ya ja kunnen jami’an ƴansanda kan take hakki da ma aikata wasu laifukan.
Egbetokun a lokacin wani taro ta intanet ya ce an kawo mishi ƙorafe ƙorafe kan take hakki da dama ta kafofin da rundunar ke karbar korafi, inda ya yi gargaɗin cewa ba za su lamunci take haƙƙin bil’adama ba kuma wanda aka kama zai fusknaci hukunci mai tsauri.
Cikin wata sanarwa da kakakin rundunar, Muyiwa Adejobi ya fitar, Egbetokun ya kuma gargaɗi jami’ai na musamman kan wuce gona da iri da kuma yin shigar da ba ta dace ba, inda ya jaddada muhimmancin sanya kayan da suka dace a lokacin aiki tare da haramta wa duk wanda ke sanye da kayan gida ɗaukar makami.
Sufeton ƴansanda ya kuma buƙaci jam’ian tsaron a kowane matsayi su yi aiki tare domin kauce wa duk wani abu da zai ɓata musu suna.