Tawagar kwallon kafa ta Nigeria ta kai zagaye na biyu a gasar cin kofin nahiyar Afirka, bayan cin Guinea-Bisau 1-0 ranar Litinin.
Wasa na uku-uku a cikin rukunin farko da aka buga kenan, inda a lokacin Equatorial Guinea ta caskara Ivory Coast 4-0.
Najeriya ta zura kwallo ne a minti na 36, bayan da Guinea ta ci gida ta hannun Opa Sangante.
Super Eagles ta ci kwallo biyu ana sokewa, ita ma Guinea-Bissau ta zura kwallo a ragar Nageriya, amma ba a karɓa ba.
Da wannan sakamakon Super Eagles ta kare a mataki na biyu a rukunin farko da maki bakwai, yayin da Equatorial Guinea ce ta yi ta ɗaya da maki bakwai iri ɗaya da na Najeriya.
Ivory Coast ta sha kashi a hannun Equatorial Guinea da ci 4-0 a ɗaya karawar rukunin farko.
Kai tsaye Equatorial Guinea ce ta ja ragamar rukunin farko da maki bakwai sai Najeriya ta biyu ita ma mai maki bakwai.
Tun a baya Equatorial Guinea ta ƙasa haura wasannin rukuni a gasar cin kofin Afirka biyu, amma ta ja ragamar rukunin farko a Ivory Coast.