Ta Inda Baki Ya Karkata Ne Ya Sanya Sheik Aminu Daurawa Ajiye Mukaminsa

Spread the love

Fitaccen malamin addinin Musulunci a Kano, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa, ya yi murabus daga muƙaminsa na shugaban hukumar Hisbah a jihar.

Murabus ɗin malamin na zuwa kwana guda bayan da gwamnan jihar, Abba Kabir Yusuf ya nuna damuwarsa kan salon da hukumar Hisbah ke bi wajen yaƙi da masu aikata baɗala a Kano.

A wani bidiyo mai tsawon ƙasa da minti uku da Sheikh Daurawa ya wallafa a shafinsa na Facebook, malamin ya bayyana cewa kalaman gwamnan sun kashe masa gwiwa kuma a don haka ya ajiye muƙaminsa na jagora a hukumar ta Hisbah.

Daurawa ya ce “Mun yi iya ƙoƙarinmu domin yin abin da ya kamata, to amma ina bai wa mai girma gwamna haƙuri bisa fushi da ya yi da maganganu da ya faɗa. Kuma ina roƙon ya yi mani afuwa na sauka daga wannan muƙami da ya bani na shugabancin Hisbah.”

A ƴan kwanakin da suka gabata ne, Hisbah ta kama shahararriyar ƴar tiktok ɗin nan, Murja Ibrahim Kunya bisa zargin aikata baɗala a jihar Kano lamarin da hukumar ta ce ke lalata tarbiyyar matasa.

An Maka Alƙali A Kotu Kan Rushe Gidan Marayu A Zariya

Gwamnatin Kano ta fitar da sabon umarni ga Sarakuna

Hukumar ta kuma aika ta zuwa kotu wadda kuma ta tura ta gidan gyaran hali.

Bayan an aika ta gidan gyaran hali ne kuma aka wayi gari da labarin sakinta daga kurkuku, abin da ya yi ta tayar da ƙura a tsakanin al’ummar jihar inda wasu ke ganin da hannun gwamnati a sakin nata – zargin da gwamnatin ta musanta.

A yanzu dai Murja Kunya na asibitin masu larurar ƙwaƙwalwa bisa umarnin kotu domin gwada lafiyar ƙwaƙwalwarta. Kotun ta ce ƴar Tiktok ɗin za ta yi wata uku a can.

Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf da yake jawabi a wani taro da ya yi da limaman Kano a gidan gwamnatin jihar ya ce sai hukumar Hisbah ta ɓuge da aikata wasu abubuwa da ba su dace ba.

Gwamnan ya ce ya ga wani bidiyo da ya tayar masa da hankali, na yadda ma’aikatan hukumar ke kama waɗanda suke zargi da aikata laifi.

”Na ga wani bidiyo, inda ma’aikatan hukumar suka je wurin wasu matasa da ake zargi da aikata laifi, amma yadda aka ɗebo su ana dukansu da gora, suna gudu ana bin su da gora ana taɗe kafafunsu, ana ɗebo su kamar awaki a jefa su cikin mota, Allah ya kiyaye in kashin bayan wani ya karye, ya gama yawo har abada, wannan kuskure ne babba”, in ji gwamnan na Kano.

”Ka rungume matashiya ko matashi ka jefa shi kamar akuya cikin mota, wannan sam bai daidai ba ne”.

”Na ga wani bidiyo inda aka je ɗakunan ɗaliban jami’ar Bayero, har ɗakunansu ana duka ana rungumo su ana jifansu cikin mota, haƙiƙa wannan batu akwai gyara”.

Gwamnan ya ƙara da cewa dole ne hukumar ta sake salo a daburunta na yaƙi da baɗala a jihar, saboda a cewarsa an saka hukumar Hisba ne don ta yi wa addinin musulunci hidima, amma idan ta bi wannan hanya, ba za a samu gyaran da ake so ba, domin waɗanda ake ƙoƙarin su gyarun, sai su kangare.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *