Takutaha: Rundunar Yaki Da Kwacen Waya, Fadan Daba ta Baza Jami’an Ta 600 Don Ba Da Tsaro

Spread the love

Rundunar da ke yaƙi da ƙwacen Waya da faɗan Daba da kuma magance shaye-shaye ta Anti Snaching Phone, da ke jihar Kano, ta ce ta baza jami’an ta kusan 600, domin samar da tsaro ga masu fita bikin Takutaha a sassan jihar.

Kwamandan rundunar, kuma mashawarci na musamman ga gwamnan Kano akan harkokin tsaro Inuwa Salisu Sharaɗa, ne ya bayyana hakan yayin zantawar sa da manema labarai.

A ranar Lahadin nan ne dai ake bikin Takutaha, wanda ɗumbin al’umma a sassan jihar Kano suke zagayen wurare daban-daban tare da ziyarce-ziyarce, har ma da zuwa kan Dutsen Dala, wuri mai ɗumbin Tarihi, a wani ɓangare na murnar zagayowar ranar sunan Ma’aiki Sallallahu alaihi Wasallama.

Inuwa Sharaɗa, ya kuma ce jami’an su na farin kaya da ma masu sanye da Kaki za su shiga lungu da saƙo a jihar Kano, domin ganin an gudanar da bikin Takutahar cikin kwanciyar hankali.

“Mun samu rahoto tare da sunayen wasu daga cikin ɓata gari da suke shirin aiwatar da mummunar ɗabi’ar da bata dace ba wajen tayar da hankalin al’umma, kuma zamu yi duk mai yiyuwa wajen ganin mun daƙile aniyar su ba tare da sun samu nasara ba, “in ji Inuwa”.

Ya ƙara da cewa duk wani wuri da aka san akwai ɓata gari a sassan jihar Kano, za su yi duk mai yiyuwa wajen ganin an ɗauki matakin da ya dace domin ƙara wanzuwar zaman lafiya a faɗin jihar Kano.

“Tuni gwamnan Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf, ya bamu umarni domin mu daƙile duk wani abu da ka iya tayar da hankalin al’umma, musamman wajen daƙile, faɗan Daba, ƙwace waya, da sauran Laifuka, kuma a shirye muke domin magance matsalolin, “in ji shi”

Ya ce duk wanda ya ga faruwar wani abu da ka iya haifar da matsalar tsaro zai iya sanar da su ta wannan lambar 08137261928, domin kai ɗaukin gaggawa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *