Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta jihar Kano ta bankaɗo wata m’ajiya da aka karkatar da shinkafar da gwamnatin tarayya ta bayar a matsayin tallafi don raba wa talakawa.
An gano cewa ana sauya buhun shinkafar wacce ta kai tirela 28 domin siyar da ita a kasuwa.
Shugaban hukumar karbar korafe-korafe da yaki da cin hanci da rashawa na jahar, Barista Muhuyi Magaji Rimingado, ne yabayyana hakan ga manema labarai , Inda ya ce yanzu haka an kama mutum daya Kum za a ci gaba da bincike don gano sauran masu hannu a cikin laifin.