Sabon Kwamishinan yan sandan jahar Kano, CP Salman Dogo Garba, ya Kama aiki a matsayin Kwamishinan yan sandan jahar na 46 a Ranar Litinin 24 ga watan Yuni 2024.
CP Salman Dogo, an haife a Ranar 21 ga watan Yuli 1966, a Karamar hukumar Ilorin ta Yamma dake jahar Kwara.
Ya Fara karatunsa a makarantar primary ta Al-Mubarak Ilorin , Teachers College Kogi da kuma jam’ar Ahmadu Bello Zaria (A.B.U.).
Haka zalika ya shiga makarantar horas da Jami’an yan sanda ta Wudil Kano, a shekarar 1992, sannan ya Fara aiki a ofishin yan sanda na Garki Abuja, a shekarar 1994.
Daga shekarar 1995 zuwa 2014 , ya rike matsayi a wurare daban-daban, da Suka hada da ,
i. Divisional Crime Office (DCO), Gwagwalada Division, FCT Police Command
ii. Officer in Charge of Special Anti-Robbery Squad (O/C SARS), FCT Police Command
iii. Divisional Police Officer (DPO) in several Divisions in FCT, Delta and Osun State Police Command.
iv. Staff Officer Senior (SOS), FCT Police Command
v. Second in command at the Department of Operations, Delta State Police Command
vi. Chief Superintendent of Police, Department of Finance and Administration (CSP ‘A’), Delta State Police Command
vi. Officer in Charge of State Intelligence Bureau (O/C SIB), Delta State Police Command.
- Ana yi mana zagon ƙasa a harkar man fetur – Dangote
- Al’ummar Ogurute Oombe sun miƙa sabon asibiti ga gumaka don samun kariya a Enugu
A shekarar 2014, ya samu Karin girma zuwa mataimakin Kwamishinan yan sanda, sannan a shekarar 2019, ya samu matsayin Kwamishinan yan sanda.
A shekarar 2022, ya samu Karin girma zuwa Kwamishinan yan sanda , Kafin a turo shi jahar Kano a matsayin Kwamishinan yan sanda na 46.
CP Salman D Garba, ya halacci kwasa-kwasai da taron Kara wa juna sani, a gida Nigeria da kuma kasashen ketare.
i. Community Policing Course in USA in the year 2008
ii. Advance Detective Course at Police Staff College, Jos in the year 1999
iii. Intermediate Command Course at Police Staff College Jos in the Year 2007
iv. Advance Intelligence and Analysis Course at Nigeria Military School of Intelligence, Apapa Lagos in the year 2010
v. Strategic Leadership Command Course at Police Staff College Jos in the year 2018, etc.
Sabon Kwamishinan yan sandan Kanon, ya Yi aiki a shiyoyin Nigeria 6, Wanda ya samu gogewa a harkar Tsaro.