Gwamnatin jahar Kano, ta musanta labarin da ake yada wa kan wani dan jarida da harsashin bindiga ya same shi, a gidan gwamnatin jahar a ranar juma’ar da ta gabata.
Mai magana da yawun gwamnan jahar Kano, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya ce an jawo hankalin gwamnatin jihar , kan wani rahoton da ya fito daga kafafen yada labaran yanar gizo da ke nuna cewa wani harsashi ya sami wani dan jarida dake wakiltar gidan talabijin din ARTV a gidan gwamnatin jihar.
Dawakin Tofa, ya bayyana hakan ne ta cikn wata sanarwa da ya fitar, a ranar Asabar inda ya bayyana lamarin a matsayin mara tushe balle makama.
- Kotu Ta Tsare Mutane 2 Bisa Zargin Damfara Da Bayar Da Cin Hannci Ga Jami’an Yan Sanda A Ekiti.
- Kotu Ta Yanke Wa Tsohon Manajan Bankin FCMB Hukuncin Shekaru 121 Saboda Da Damfarar 112.1m
Sanarwar ta kara da cewa, ba harsashi ne ya samu wakilin gidan Talabijin na ARTV ba, ya samu raunukan ne ta tarkacen karafuna da aka fito da su daga wani gini da ake gyarawa a fadar gwamnatin Kano.
An kai Naziru Idris Ya’u, a asibitin fadar gwamnatin jahar inda aka bashi kular lafiya a hannunsa sakamakon raunukan da ya samu, inda lamarin ya girgiza yan jarida ciki da wajen jahar Kano.
Tunda fari da wasu rahotanni na cewa harsashin bindiga a fadar gwamnatin Kano ya jikkata dan jaridar mai suna Naziru Idris Ya’u dake aikin da gidan talabijin din ARTV Kano.