Tattalin arzikin Najeriya ya ƙara lalacewa a ƙarƙashin Tinubu – Atiku

Spread the love

Tsohon mataimakin shugaban Najeriya kuma jagoran adawa a Najeriya, Atiku Abubakar, ya caccaki gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ta APC, yana mai cewa sauye-sauyen tattalin arziki da ta ɗauka ba su sauƙaƙa wa ‘yan ƙasa wahalhalu ba cikin shekara ɗaya.

Jim kaɗan bayan rantsar da shi a kan mulki, Tinubu ya ƙaddamar da wasu jerin sauye-sauye da zimmar farfaɗo da tattalin arziki, waɗanda daga baya suka haddasa hauhawar farashi da kuma ƙunci a ƙasar baki ɗaya.

Atiku ya ce tattalin arzikin ma baya ya koma a cikin shekara ɗaya ta mulkin Tinubu.

“Kamar yadda muka yi tsammani, cikin wata 12, Tinubu bai cka alƙawarin farfaɗo da tattalin arziki da kawo ƙarshen wahalhalu ba,” in ji shi cikin wata sanarwa da ya wallafa.

“Matakan da ya ɗauka da waɗanda bai ɗauka ba sun ƙara ta’azzara tattalin arzikin Najeriya. Har yanzu ƙasar na fama kuma ta ma fi tangal-tangal a yanzu sama da shekara ɗaya da ta wuce.

“Tabbas duka matsalolin – rashin aikin yi, da talauci, da wahalhalu – da suka mamaye gwamnatin Buhari sun ƙara ta’azzara.”

Idan ba a manta ba, daga cikin manyan matakan da Tinubu ya ɗauka har da sanar da cire tallafin man fetur a jawabinsa na rantsuwar kama aiki, kodayake rahotonni na cewa har yanzu gwamnati na biyan tallafin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *