Taurin bashi ya sanya babbar kotun tarayya bada umarnin rufe asusun gwamnatin jahar Kano

Spread the love

Wata babbar kotun tarayya da ke zaman ta a birnin tarayya Abuja, karkashin jagorancin mai shari’a I.E. Ewo , ta bayar da umarnin rufe asusun gwamnatin jahar Kano a wasu Bankunan kasuwanci guda 20 da kuma wasu 4 a fadin Nijeriya.
Wannan dai na zuwa ne bayan wasu gungun yan kasuwa a jahar Kano , sun garazaya gaban kotun domin ta karbar mu su hakkokin su na rushe mu su shaguna ba bisa ka’ida ba.
Ma su karar sun nemi gwamnatin jahar Kano ta biya su diyar Naira Biliyan 30, da suke bin bashi.
Cikin kunshin ma su karar da suka hada , Alhaji Sani Uba, Ifeanyi Nwobodo, Alhaji Abdullahi A. Idris, Alhaji Awalu sai’du da kuma sauransu.
Tun a watan Nuwamban 2023 ne , babbar kotun tarayya dake zaman ta a Kano , ta yanke hukuncin karar da yan kasuwar suka shigar gaban ta, inda kotun ta umarci gwamnatin jahar ta biya diyar naira Biliyan 30 ga ma su shagunan da aka rushe wa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *