Shugaban Najeriya na yin wata ganawa da shugaban ƙasar Faransa Emmanuel Macron a ranar farko ta ziyarar aiki da shugaban na Najeriya ke yi a ƙasar.
A yau Alhamis, Tinubu ya isa fadar shugaban Faransa ta Elysee tare da tawagarsa, wadda ta hada da ministan harkokin wajen Najeriya, Yusuf Tugga da ministan kuɗi, Wale Edun da na tsaro Badaru Abubakar.
A ɓangare ɗaya shugaban Faransa ya shiga ɗakin taron ne tare da ƙaramin ministan harkokin waje na ƙasar, Thani Mohamed Soilihi da kuma ministan tsaro na Faransa, Sebastien Lecornu da sauran jami’ai.
Ana sa ran Najeriya da Faransa za su ƙulla hulɗoɗi na diflomasiyya da kasuwanci a lokacin ziyarar ta shugaba Tinubu, wadda take zuwa bayan ragin tagomashi da Faransa take samu a Afirka.
Dangantaka ta yi tsami tsakanin Faransa da ƙasashen da ta rena a yammacin Afirka, kamar Nijar da Burkin Faso da Mali.
Ƙasashen sun yanke huldar diflomasiyya da Yamma tare da karkata akalarsu zuwa ɓangaren Rasha.
A matsayinsa na shugaban ƙungiyar ƙasashen yammacin Afirka, Tinubu ya yi ƙoƙarin ganin ƙasashen Nijar da Mali da Bukina Faso sun koma tafarkin dimokuraɗiyya sai dai har yanzu abin ya ci tura.