Tinubu na neman mallaka wa kansa Najeriya – Atiku

Spread the love

Tsohon mataimakin shugaban Najeriya, Atiku Abubakar, ya zargi shugaba Bola Tinubu da cewa yana nemen mayar da Najeriya mallakin kansa.

Atiku, ɗan takarar jam’iyyar PDP a zaɓen shugaban ƙasa na shekarar 2023 ya yi iƙirarin cewa Tinubu yana jinginar da makoman matasan Najeriya ga kansa da iyalinsa da kuma abokansa na kusa.

Atiku ya bayyana hakan ne a wata sanarwa da mai ba shi shawara kan harkokin yaɗa labarai, Paul Ibe ya bayar a jiya Laraba, 21 ga watan Agusta inda ya bayyana damuwarsa da cewa ko bayan Tinubu ya bar mulki, zai yi wahala a warware abubuwan da ya kafa tare da kuma magance waɗannan matsalolin.

Atiku ya yi misali da yadda Tinubu ke cuɗanya harkokin kasuwancinsa a gwamnati a Legas da kuma yunƙurinsa na cusa harkokin kasuwancinsa a yanzu a cikin Gwamnatin Tarayya.

Atiku ya ce a sanarwar “na yi matuƙar mamaki da gano cewa kamfanin man fetur na Najeriya (NNPC) ya sanya ayyukansa na sayar da kayayyaki a ƙarƙashin kulawar OVH, wani kamfanin da Oando ke da kashi 49 cikin ɗari.”

“Oando fa yana ƙarkashin jagorancin Wale Tinubu ne, ƙanen Shugaban Tinubu.” in ji sanarwar.

Atiku ya bayyana baƙin cikinsa kan yadda wasu kamfanoni da ke da kusanci da Tinubu suka mamaye kamfanin NNPC ba bisa ka’ida ba.

A wani sakon da ya wallafa a shafin sa na X a ranar Litinin, Atiku ya soki gwamnatin Tinubu kan cire tallafin man fetur wanda shine tushen halin da ƴan Najeriya ke ciki.

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *