Tinubu na son tsawaita wa’adin shugaban ƴansanda har zuwa 2027

Spread the love

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya rubuta wa majalisun dokoki na tarayyar ƙasar wato majalisar wakilai da ta dattawa wannan buƙatar tsawaita amince da wani ƙudirin doka da zai riƙa bai wa Babban Sufetonn ‘yansanda damar ci gaba da zama a kujerarsa ko da lokacin ritayarsa ya yi, har sai wa’adin naɗin da aka yi masa ya ƙare.

Wannan na ƙunshe ne a cikin wata wasika da ta nemi a sauya dokar ‘yansanda ta 2020.

Cikin wasiƙar da aka karanta a zauren majalisun a ranar Talata, Shugaban ya nemi a bai wa Babban Sufeton ‘yansandan damar ya ci gaba da shugabanci ko da lokacin ritayarsa ya yi har sai wa’adin naɗin da aka yi masa ya ƙare.

Hakan na nufin Babban Sufeton ƴansandan na yanzu, Kayode Egbetakun wanda ya kamata ya yi ritaya a watan Satumba, zai ci gaba da riƙe muƙamin har sai watan Yunin 2027.

Sanata Ahmed Abdulhamid Malam Madori wanda shi ne shugaban kwamitin ‘yan sanda na Majalisar Dattijan kasar ya ce idan aka yi wa lamarin kallo na tsanaki akwai alfanu a cikinsa.

“Wannan dama ce ta shugaban ƙasa ya naɗa wanda yake ganin ya cancanta ya yi aiki da shi, ita dokar tana nufin Sufeton ƴansanda zai riƙa gama wa’adin mulkinsa tare da gwamnatin da ta naɗa shi, kuma ko a baya an sha yin hakan, sannan lokacin gwamnatin Buhari ma an tsawaita wa’adin shugaban ƴansanda,” in ji Sanata Malam Madori.

Dokar dai ta ƙunshi batun tsawaita wa’adin shugaban ƴansanda ne ƙadai ba tare da sauran shugabannin tsaro ba, “Mu abin da muka yi na ɓangaren ƴansanda ne domin ita ce buƙatar da ta zo mana,”cewar Sanatan.

Sanata Ahmed Malam Madori ya ce abin takaici ne yadda ake rasa ƙwararrun ƴansanda a ƙasar, “Kuma idan ka rasa su waɗanda suke a bayansu ba su samu horon da waɗannan masu tafiyar suka samu ba.”

Kwamred Auwal Musa Rafsanjani wanda shi ne shugaban kungiyar Sislac mai sanya ido kan ayyukan majalisu, ya ce ya kamata a sake nazarin dokar kafin a tabbatar da ita.

“Babbar matsalar shi ne hakan zai kawo rashin kwanciyar hankali a tsakanin ƴansanda, akwai da dama jami’an ƴansanda da suke jiran gado, wannan doka ta kawo ƙarshen jiran gadon da suke yi,” a cewar Rafsanjani.

Masu sharhi da yawa na ganin dokar za ta yi aiki ne kan babban sufeton ƴansandan kasar na yanzu Kayode Egbetakun wanda Tinubu ya naɗa a watan Yunin 2023 da wa’adin shekaru huɗu, wato zai kare 2027.

Amma a ƙa’idar aiki Egbetokun da aka haifa a ranar 4 ga watan Satumbar 1964 zai cika shekara 60 a watan Satumbar 2024, don haka lokacin ritayarsa ya yi, amma da wannan doka zai ci gaba da aiki har sai watan Yunin 2027.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *