Tinubu ya ƙaddamar da asusun bai wa ɗalibai bashin karatu

Spread the love

Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya ƙaddamar da asusun baiwa dalibai bashin karatu ta Najeriya (NELFund), a wani taro d aka gudanar a zauren taro na fadar shigaban ƙasa da ke Abuja

Taron ya sami halarcin shugabannin majalisar dokokin ƙasar, da sakataren gwamnatin tarayya, da wasu ministoci, da shugabannin hukumomi, da mambobin kwamitin da gudanarwa na asusun ƙarƙashin jagorancin shugaban kwamitin, Jim Ovia.

A nasa ɓangaren, Shugaban asusun ta NELFund, Akintunde Sawyerr, ya ce manhajar asusun ta karbi sama da bukatu 110,000 na ɗalibai masu neman bashin karatu.

Shirin baiwa ɗalibai bashin na neman bayar da tallafin kuɗi, wanda ya haɗa da kuɗin makaranta da na sanya wa a aljihu, ga ɗaliban da suka cancanta a duk faɗin ƙasar.

Sama da dalibai miliyan 1.2 ne ake sa ran za su ci gajiyar zango na farko a shirin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *