Shugaba Bola Ahmed Tinubu, ya kafa sabuwar Ma’aikatar Harkar Kiwon Dabbobi.
A watan Satumban 2023, Shugaba Tinubu ya amince da kafa kwamitin shugaban ƙasa don gyaran ɓangaren kiwo da magance rikice-rikicen makiyaya da manoma.
Wannan shawarar ta biyo bayan rahoton taron ƙasa kan gyara tsarin kiwo da rage rikice-rikicen da ke da nasaba da kiwo a Najeriya.
- An gano Kurar da ta tsere daga gandun dajin Jos
- Majalisar wakilan Najeriya ta nemi a dakatar da yarjejeniyar Samoa
Kungiyar Miyetti Allah ta MACBAN, ta buƙace shugaban ƙasa ya ƙirƙiro ma’aikatar kiwo.
Shugabansu, Alhaji Baba Usman Ngelzarma, ya ce makiyaya na buƙatar ma’aikata mai zaman kanta da za ta kula da dukkanin al’amuran da suka shafi kiwo.
Ngelzarma ya bayyana cewa samun ma’aikatar zai magance dukkanin sarƙaƙiyar da ta shafi kiwo, kamar kasuwanci, sufuri da tsaro, maimakon mai da hankali kawai kan kiwo.