Tinubu Ya Amince Da N70,000 A Matsayin Mafi Ƙarancin Albashi

Spread the love

ShugabaN kasa Bola Ahmed Tinubu ya amince da Naira 70,000 a matsayin sabon mafi ƙarancin albashin ma’aikatan Nijeriya.

Ministan Labarai, Mohammed Idris ne ya sanar hakan yau Alhamis yayin ganawa da manema labarai a Fadar Shugaban Kasa da ke Abuja.

Ministan ya ce Shugaba Tinubu ya kuma ƙuduri aniyar bitar dokar albashi mafi ƙaranci duk bayan shekara uku.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *