Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu ya ayyana dokar ta-ɓaci a jihar Rivers bayan rikita-rikitar siyasa da jihar ta daɗe tana fama da shi tare da kuma da naɗa wanda zai riƙe muƙamin gwamnan jihar na tsawon wata shida.
Shugaban ya ayyana hakan ne a jawabin da ya gabatar a kan ruɗanin siyasar da ke addabar jihar ta Rivers, wanda ya ƙi ci ya ƙi cinyewa.
Gwamnan jihar Siminalayi Fubara da majalisar dokokin jihar sun kasa samun fahimtar juna kusan tun bayan hawansa kan mulki, duk kuwa da hukunce-hukunce da kotu ta zartar.
A cikin jawabin da ya gabatar ta kafafen talabijin na ƙasar, shugaban Najeriya Bola Tinubu ya ce: ”Bayan nazari kan halin da ake ciki a jihar Rivers, ya zama wajibi na yi amfani da sashe na 305 na kundin tsarin mulkin Najeriya na 1999.
“A kan haka, na ayyana dokar ta-ɓaci daga yau 18 ga watan Maris, 2025.”
Shugaban ƙasar ya ƙara da cewa ”Matakin na nufin an dakatar da gwamnan Siminalayi Fubara da mataimakiyarsa Farfesa Ngozi Odu na tsawon wata shida”.
”Na yi iyakar bakin kokarina wajen ganin yadda za a magance matsalar to amma duka ɓangarorin sun yi watsi da yunkurin.”
Haka nan shugaban ƙasar ya bayyana cewa wasu mutane daga ɓangarori daban-daban su ma sun yi nasu kokarin amma an kasa samun mafita.
”A yanzu ta tabbata babu wata sahihiyar gwamnati a jihar Rivers.” in ji shugaba Tinubu.