Tinubu ya buƙaci a hukunta wanda ya cinna wa masallaci wuta a Kano

Spread the love

Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya buƙaci hukumomin tsaro su tabbatar an yi kyakkywan bincike tare da hukunta duk wanda ke da hannu a cinna wuta a masallaci wanda ya yi sanadiyyar hasarar rayuka a jihar Kano.

A cikin wata sanarwa da ta fito ta hannun mai magana da yawun shugaban ƙasar, Ajuri Ngelale, a yau Talata, Tinubu ya jajanta wa mutanen da suka rasa ƴan uwansu sanadiyyar lamarin da kuma yin addu’ar waraka ga waɗanda suka samu rauni.

Wani matashi mai shekara 39 a makon da ya gabata ya cinna wa masallaci wuta a ƙauyen Larabar Abasawa da ke ƙaramar hukumar Gezawa ta jihar Kano.

Lamarin ya yi sanadin rayukan mutum 17 yayin da dama ke ci gaba da jinya a asibiti.

Tuni dai aka gurfanar da wanda ake zargi a wata kotun shari’ar musulunci da ke birnin Kano a ranar Litinin.

Duk da cewa wanda ake zargin ya amsa laifinsa, alƙalin kotun ya ɗage shari’a zuwa ƙarshen wannan wata na Mayu domin bai wa wanda ake zargi damar ɗaukar lauya da kuma bai wa masu ƙara damar agabatar da shaidu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *