Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya gana da gwamnonin ƙasar a zauren majalisar dokoki da ke Abuja.
Taron wanda aka fara da misalin karfe 11:30 na safe, ya samu halartar mataimakin shugaban ƙasa Kashim Shettima da ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike; da Sufeto Janar na ‘yan sanda, Kayode Egbetokun.
Taron dai bai rasa nasaba da damuwar da ake nunawa a fadin kasar dangane da tsadar kayan abinci da rashin tsaro da sauran batutuwan da suka shafi tattalin arziki.
Taron dai ya biyo bayan taron Majalisar Tattalin Arzikin Kasa (NEC) na wata-wata, wanda mataimakin shugaban kasa Shettima ya jagoranta.
Bayan koke-koke da al’ummar kasar suka yi kan tabarbarewar tsaro da tabarbarewar tattalin arziki, shugaban kasar ya umarci ma’aikatar noma da samar da abinci ta saki kimanin tan dubu arba’in da biyu na masara da gero da sauran kayayyakin masarufi a cikin tsare-tsare don magance hauhawar farashin kayan abinci a kasar.
Kaunar Murja Kunya ya ratsa cikin zuciya ta don haka ku Aura mun ita: Ustaz Assalafi
Shugaban ya kuma tabbatar da cewa zai ci gaba da zuba ido kan ƙalubalen tattalin arziƙi da tsaro da Nigeria ke fuskanta.
Fadar shugaban kasa ta bayyana cewa sauye-sauyen tattalin arziki da gwamnatin Tinubu ta yi ciki har da cire tallafin man fetur ya zama dole, inda ta kara da cewa wadannan matakan za su haifar da riba nan ba da jimawa ba.