Tinubu ya gana da manyan hafsoshin tsaro

Spread the love

Shugaba Bola Tinubu ya gana da hafsoshin tsaron Najeriya da kuma wasu manyan hukumomin tsaro a fadarsa da ke Abuja, a yau Talata.

Hafsoshin tsaron da suka halarci ganawar sun haɗa da babban hafsan tsaro, Janar Christopher Musa, shugaban rundunar sojin ƙasa, Laftanar-Janar Taoreed Lagbaja, shugaban sojin sama, Air Marshal Hassan Abubakar, da kuma shugaban sojojin ruwa, Vice Admiral Emmanuel Ogalla.

Shi ma mai taimakawa shugaban ƙasa kan harkokin tsaro, Malam Nuhu Ribadu na cikin waɗanda suka halarci taron.

Sun tattauna kan batun ƙaruwar aikata ta’addanci, garkuwa da mutane da kuma kashe-kashe a faɗin ƙasar da nufin magance su.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *