Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya gana da sabon shugaban Senegal Bassirou Diomaye Faye, a ziyarar farko da sabon shugaban ƙasar ya kai Najeriya.
A ranar biyu ga watan Afrilu ne aka rantsar da Bassirou Faye a matsayin zaɓaɓɓen shugaban ƙasa mafi ƙarancin shekaru a Afirka bayan nasarar da ya yi a zaɓen ƙasar da aka gudanar.
Faye ya lashe zaɓe ne bisa alƙawurra da ya yi na kawo gagarumin sauyi a ƙasar.
Matsalar ƙarancin aikin yi da rashin kyawun tattalin arziƙi ne manyan matsalolin da ke addabar ƙasar ta Senegal.
- Majalisar dattijan Najeriya na so a bai wa ƙananan hukumomi ƴancin kai
- Shugaban Rasha Ya Isa Kasar Sin Don Ziyarar Aiki Da Zumunci