Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya bayyana farin ciki a kan nasarar da dakarun sojin ƙasar ke samu a kan ƴan bindiga a yankin Arewa Maso Yamma.
Wata sanarwar da kakakin shugaba Tinubu, Bayo Onanuga ya fitar a ranar Asabar ta ce nasarar da dakarun ke samu wani tabbaci ne cewa za su iya aikin wanzar da tsaro a faɗin ƙasar.
A ranar Alhamis dakarun Operation Hadarin Daji suka kashe riƙaƙƙen ɗan bindiga Halilu Sububu, wanda ya daɗe yana addabar jama’a a jihar Zamfara da Sokoto da kuma wasu sassan arewacin Najeriyta.
Dakarun sun kuma yi nasarar kashe wani ɗan bindigar mai suna Sani Wala Burki a wani samemen haɗin gwiwa da suka kai maɓoyar ƴan bindiga a Katsina da kuma Kaduna, inda suka ceto mutanen 13 da aka yi garkuw ada su.
Fadar shugaban Najeriyar ta ce nasarar da sojojin ƙasar ke samu ta biyo bayan umarnin da shugaba Tinubu ya bai wa manyan hafsoshin ne na su koma yankin Arewa maso Yamma da zama har sai an samu tsaro a yankin.
Shugaba Tinubu ya kuma bayar da tabbacin cewa zai ci gaba da tallafawa jami’an tsaron ƙasar domin cimma nasarar samar da tsaro ga jama’a.