Shugaban Najeriya, Bola Tinubu ya koka kan yadda ake yi wa ƴan Najeriya kuɗin goro da sunan masu aikata laifuka ta intanet.
Ya ce irin wannan yana ɓata sunan akasarin al’ummar Najeriya da suke masu bin doka da oda. A cewar shugaban, an shafe tsawon shekaru ana yi wa ƴan Najeriya mummunar fahimta.
Shugaba Tinubu wanda ke birnin Paris na Faransa ya faɗi haka ne cikin wani jawabi da mataimakinsa Kashim Shettima ya gabatar.
Daga farkon shekarun 2000, ana kallon ƴan Najeriya a matsayin masu aikata ta’annati ta intanet – daga kutse da neman soyayya don samun kuɗi.
Kano: Kotu ta bayar da belin Danbilki Kwamanda
EFCC na bincike kan yarjejeniyar Nigeria Air – Keyamo
Tinubu ya ƙara da cewa alaƙanta laifukan intanet da al’ummar Najeriya ba shi da hujja kuma ba ya nuna yadda rayuwar ƴan Najeriya take waɗanda aka san su a matsayin jajirtattu da gaskiya sannan suna bayar da gudumawa ga ci gaban kasashe ta fannoni da dama daga batun ƙirƙirarriyar basira zuwa ga fannin lafiya.
A 2020 ne, hukumar binciken manyan laifuka a Amurka, FBI ta saka Najeriya a matsayin ta 16 a jerin ƙasashen da laifukan intanet ya fi shafa.
Laifukan intanet na janyo wa Najeriya asarar dala miliyan 500 kowace shekara, kamar yadda hukumar kula da harkokin sadarwa a Najeriya ta bayyana.