Tinubu ya rage yawan masu rakiya a tafiye-tafiyensa

Spread the love

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ba da sanarwar rage yawan jami’an da za su riƙa yi masa rakiya a duk tafiye-tafiyen aiki da zai je ciki da wajen ƙasar.

Matakin ya shafi dukkan ministoci da manyan jami’an gwamnatinsa ciki har da mataimakin shugaban ƙasa da uwargidan shugaban ƙasa.

Sanarwar wadda Ajuri Ngelale, mashawarci na musamman ga shugaban Najeriya kan harkar yaɗa labarai ya fitar ranar Talata na cewa matakin, wani yunƙuri ne na rage yawan kuɗaɗen da jami’an gwamnati ke kashewa kan harkokin tafiye-tafiye.

Ta ce yawan jami’an da za su riƙa yi wa shugaban ƙasa rakiya zuwa ƙasashen waje, nan gaba ba za su wuce jami’ai 20 ba. Haka zalika, Ngelale ya ce Tinubu ya ba da umarnin a daina tura ɗumbin jami’an tsaro zuwa wata jiha a duk lokacin da zai kai ziyara can, maimakon haka za a riƙa amfani da jami’an tsaron da ke jihar ne kawai don tabbatar da tsaro.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *