Tinubu ya sa hannu kan dokar bai wa ɗalibai bashin karatu

Spread the love

Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu, ya sa hannu kan dokar bai wa ɗalibai bashin karatu.

Ya sa hannu kan dokar ce a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja, babban birnin Najeriya.

Dokar mai taken kudurin sauya wa dokar bai wa dalibai rancen karatu fasali ta 2024, an samar da ita ne domin kafa asusun tallafa wa daliban makarantun gaba da sakandire.

A watan Nuwambar shekarar da ta wuce ne majalisar dokokin kasar ta amince da kudurin dokar, da ke neman kafa wata gidanauniyar da za ta rika ba daliban manyan makarantun kasar bashin kudin makaranta.

Sabuwar dokar dai ita ce irinta ta farko a Najeriya kuma in ji shugaban ma’aikata na Fadar Shugaban Kasar Femi Gbajabiamila, wanda shi ne ya kawo kudurin dokar lokacin yana kakakin majalisa, za ta inganta kasar domin babu wani yaron Najeriya da za a hana wa damar samun ilmi mai zurfi saboda rashin kudi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *