Shugaba Bola Tinubu ya sallami Shugaban Hukumar Alhazai ta Najeriya (NAHCON), Malam Jalal Arabi.
Sallamar tasa na zuwa ne bayan zargin shugaban da yin sama da fadi da wani ɓangare na naira biliyan 90 da gwamnatin Najeriya ta ba hukumar a matsayin tallafi ga aikin hajjin 2024 da ya gabata.
Wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban Ajuri Ngelale ya fitar, ta kuma tabbatar da naɗa Farfesa Abdullahi Saleh Usman a matsayin sabon shugaban hukumar ta alhazan Najeriya.