Tinubu ya samu tarba da sabon taken Najeriya a majalisar dokokin ƙasar

Spread the love

Shugaban Najeriya, Bola Tinubu ya isa majalisar dokokin ƙasar, domin ƙaddamar da ayyuka tare da yi wa majalisar jawabi a wani ɓangare na cikarsa shekara guda a kan mulki.

Haɗakar majalisar dattawa da ta wakilan ƙasar ne suka tarbi shugaban a wani zaman haɗin gwiwa da majalisun biyu suka gudanar.

Majalisar ta tarbi shugaban ƙasar, da tsohon taken ƙasar wanda kuma a yanzu aka aka sake dawo da shi.

A wannan makon ne majalisar dokokin da amince da ƙudirin dokar komawa amfani da tsohon taken na Najeriya.

Shugaban Majalisar dattawan ƙasar, Godswill Akpabio ya ce da safiyar yau Laraba ne shugaban ƙasar ya saka hannu kan dokar komawa amfani da tsohon taken ƙasar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *