Tinubu ya sanya wa jami’an gwamnati takunkumin fita waje na wata uku

Spread the love

Shugaban Najeriya, Bola Tinubu ya sa haramcin tafiye-tafiye zuwa ƙasashen waje tsawon wata uku ga ministoci da shugabannin ma’aikatu da hukumomin gwamnati.

Shugaban ma’aikata a fadar shugaban ƙasa, Femi Gbajabiamila ne ya sanar da umarnin cikin wata takarda da aka aikewa sakataren gwamnatin tarayya, George Akume.

An bayyana ƙalubalen tattalin arzikin da ake fama da shi da buƙatar alkinta kuɗin gwamnati da ake kashewa yayin irin waɗan nan tafiye-tafiye a matsayin dalilan da suka sa aka ƙaƙaba haramcin kan tafiye-tafiye zuwa ƙasashen waje.

Takardar ta ce jami’i na buƙatar amincewar shugaban ƙasa idan yana son a ɗage masa haramcin kuma dole a yi hakan mako biyu kafin lokacin tafiyar.

Matakin na zuwa ne bayan bulaguron baya-bayan nan da ofishin akanta janar na ƙasa ya yi da ta janyo cece-kuce.

Ofishin ya gudanar da wani taron ƙarawa juna sani a birnin Landan wanda ya samu halartar kwamishinonin kuɗi da jami’ai daga ofishin akanta janar.

Ƴan Najeriya dai sun yi ta tsokaci a kai, abin da suka ce ya zo ne a lokacin da ƙasar ke fuskantar ƙalubalen tattalin arziki da kuma tashin dala da ke shafar darajar kuɗin naira.

Majalisa ta amince ta ƙudurin sabon albashi ga alƙalan Najeriya

Wani mutum ya makanta bayan amfani da fitsari don maganin ciwon ido

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *