Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya sauke shugaban hukumar ‘yansandan farin kaya ta DSS, Yusuf Bichi, tare da maye gurbinsa da Adeola Oluwatosin Ajayi a matsayin shugaban hukumar.
Kazalika, shugaban ya naɗa Mohammed Mohammed a matsayin shugaban Hukumar Leƙen Asiri ta Ƙasa (NIA) domin ya maye gurbin Ahmad Rufai Abubakar, wanda ya ajiye aikinsa a ƙarshen mako.
Wata sanarwa da kakakin fadar shugaban ƙasa, Ajuri Nglale, ya fitar ta ce Mohammed ya fara aiki da NIA tun 1995 kuma ya yi karatu a Jami’ar Bayero da ke Kano.
Mista Adeola kuma shi ne mataimakin shugaban hukumar kafin naɗin nasa a yanzu.