Tinubu ya taya Mahamat Déby murnar lashe zaɓen Chadi

Spread the love

Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya taya zaɓaɓɓen shugaban ƙasar Chadi, Mahamat Déby murnar nasarar lashe zaɓen shugaban ƙasar da aka gudanar a makon da ya gabata.

Cikin wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban ƙasar, Ajuri Ngelale ya fitar, shugaba Tinubu ya ce nasarar gudanar da zaɓen da aka yi a ƙasar ya nuna irin kishin da al’umma da gwamnatin Chadi ke da shi wajen mayar da ƙasar kan tsarin mulkin dimokraɗiyya.

Shugaban na Najeriya ya kuma tabbatar wa da zaɓaɓɓen shugaban Chadin cewa Najeriya za ta ci gaba da aiki kafaɗa da kafaɗa da ƙasar, a yayin da ya ce duka ƙasashen biyu ke naman bunƙasa zaman lafiya da tsaro da ci gaba al’umomin ƙasashen.

Sanarwar ta kuma ce shugaba Tinubu ya yi kiran ci gaba da aiki tare da haɗin kai tsakanin ƙasashen biyu.

Shugaba Tinubu ya kuma yi fatan alƙairi ga Mahamat Déby a tsawon wa’adin mulkinsa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *