Tinubu ya taya Sheikh Dahiru Bauchi murnar cika shekara 100

Spread the love

Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya taya babban malamin addinin musulunci Shiekh Dahiru Bauchi murnar cika shekara 100 a duniya.

A sanarwar da fadar shugaban ta fitar, Bola Tinubu ya bayyana Shehin malamin a matsayin wani haske da ya yi wa addinin musulunci hidima da kuma yin tasiri ga tarbiya da tsari a Najeriya

Ya kuma gode wa babban malamain na darikar Tijjaniyya kan sadaukar da rayuwarsa wajen yaɗa ilimi da kuma tasiri ga rayuwar ƴan Najeriya.

Shugaba Tinubu ya yi addu’ar ƙoshin lafiya da ƙarin hikima ga malamin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *