Tinubu ya umarci ma’aikatar shari’a da majalisa su yi gyara a dokar haraji

Spread the love

Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya bai wa ma’aikatar shari’a umarnin yin aiki tare da majalisar dokokin ƙasar wajen gyara abubuwan da mutane ke suka game da ƙudirin gyaran dokar haraji.

Ƙudirorin huɗu sun jawo suka iri-iri daga kowane lungu da saƙo na Najeriya, musamman arewaci, tun daga lokacin da aka kai su gaban majalisa domin neman amincewarta.

“Shugaba Tinubu na maraba da duk wani gyara da zai sauya duk wata saɗara da ke jawo cecekuce a ƙudirin,” a cewar Ministan Yaɗa Labarai Mohammed Idris cikin wata sanarwa a yau Talata.

Tuni rukunin ‘yanmajalisa daga arewacin Najeriya suka ce sun yanke shawarar yin watsi da ƙudirin, wanda tuni ya tsallake karatu na biyu, a majalisar dattawa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *