Tinubu zai fara bikin cika shekara guda a mulki da buɗe ayyuka a Legas

Spread the love

Shugaban Najeriya, Bola Tinubu zai fara bikin murnar cikarsa shekara guda a kan karagar mulkin ƙasar da buɗe wasu muhimman ayyukan gwamnatin Tarayya a Legas da aka kammala a lokacin mulkinsa.

Cikin wata sanarwa da mataimaki na musamman ga shugaban kan kafofin yaɗa labarai na zamani, Bayo Onanuga ya fitar, ya ce a yau Lahadi shugaba Tinubu zai buɗe wani babban titin da aka yi da kankare zuwa manyan tasoshin jiragen ruwa na Apapa da Tin Can a birnin na Legas.

Sanarwar ta ce an fara muhimmin aikin titin ne a zamanin tsohuwar gwamnati Muhammadu Buhari da ta gabata, inda kamfanin Dangote ya ɗauki nauyi gudanar da aikin ta hanyar harajin da yake tara wa gwamnati.

”Haka kuma shugaba Tinubu zai buɗe fitacciyar gadar nan ta ‘Third Mainland’ da ta ɗauki hankali sakamakon yadda aka zamanantar da ita”, in ji Sanarwar.

”Shugaban ƙasar zai kuma ƙaddamar da katafaren aikin titin da ya tashi daga Legas zuwa Calaba da aka yi ƙiyasin cewa zai laƙume kusan naira tiriliyan 15, muhimmin titi ne da zai ratsa jihohin kudancin ƙasar aƙalla tara”, kamar yadda Bayo Onanuga ya bayyana.

Haka kuma sanarwar ta ce shugaban ƙasar zai ƙaddamar da aikin sake gina tituna har 330 a duka faɗin ƙasar.

Sanarwar ta kuma ƙara da cewa a ranar Talata shugaban ƙasar zai koma koma Abuja babban birnin ƙasar, inda a nan ma ya tsara ƙaddamar da ayyuka ciki har da fara jigilar jirgin ƙasan fasinja da zai riƙa zagaya birnin Abuja.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *