Tinubu zai yi wa ‘yan majalisa jawabi a bikin dimokuraɗiyya

Spread the love

Shugaban Najeriya Bola Tinubu zai yi wa zaman haɗin gwiwa na majalisar ƙasar jawabi gobe Laraba a wani ɓangare na bikin cika shekara 25 da ɗorewar mulkin dimokuraɗiyya ba tare da katsewa ba.

Akawun Majalisa Sani Tambawal ya ce shugaban zai kuma ƙaddamar da wani sabon ɗakin karatu da aka gina a farfajiyar ginin majalisar.

“Ana sanar da sanatoci da wakilai cewa a wani ɓangare na bikin cika shekara 25 na mulkin dimokuraɗiyya da wakilci a majalisa, za a yi zaman haɗin gwiwa tsakanin majalisar wakilai da ta dattawa ranar Laraba,” a cewar wata sanarwa.

A ranar 29 ga watan Mayun 1999 aka rantsar da Olusegun Obasanjo a matsayin shugaban ƙasa zaɓaɓɓe, wanda ke nufin an shiga jamhuriya ta huɗu a siyasar Najeriya, kuma tun daga lokacin mulkin dimokuraɗiyya bai sake gamuwa da tangarɗa ba.

Sai dai a yanzu ana bikin Ranar Dimokuraɗiyya ne ranar 12 ga watan Yuni tun daga 2018 – lokacin da tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya sauya ta daga 29 ga watan Mayu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *